Mummunan hatsarin mota a Bolibiya

Mutane 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a lokacinda motar bas ta yi taho mu gama da akori-kura a kasar Bolibiya.

Mummunan hatsarin mota a Bolibiya

Mutane 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a lokacinda motar bas ta yi taho mu gama da akori-kura a kasar Bolibiya.

'Yan sanda sun bayyana cewa, a hanyar da ta hada yankunan Potosi da Oruro ne hatsarin ya afku inda wasu karin mutane 12 suka samu raunuka.

An bayyana cewar yawaitar hazo ne ya janyo afkuwar hatsarin.

A watan da ya gabata ma a wannan hanyar wani hatsarin mota ya afku tare da yin sanadiyyar mutuwar mutane 22.Labarai masu alaka