Taron kolin G20 da kisan Kashoggi

A sanadiyar taron ƙolin ƙasashen G20 shugabanin ƙasashen duniya suka taru a babban birnin ƙasar Argentina inda suka tattauna akan muhimman abubuwa.

Taron kolin G20 da kisan Kashoggi

A sanadiyar taron ƙolin ƙasashen G20 shugabanin ƙasashen duniya suka taru a babban birnin ƙasar Argentina inda suka tattauna akan muhimman abubuwa. Baya ga ganawar da shugabannin suka yi da juna an kuma tattauna akan rikicin kasuwanci dake tsakanin Amurka da China tare da taɓo batun kashe ɗan jaridar Washington Post Jamal Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya dake lstanbul, lamarin da ake zargin yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman da bayar da umurnin aikatawa.

      Kamar ko wacce sati, a wannan makon ma mun sake kasancewa tare da masanin ilmin siyasa Mal Yazar Can ACUN daga cibiyar nazarin siyasa da tattalin arziki wato SETA.

               Kasancewar yadda shugabannin da hukumomin ƙasar Turkiyya har ma dana ƙasa da ƙasa suka dauki kwararan matakai bayan kashe Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya dake lstanbul ya sanya ƙasar Saudiyyar bayyana gaskiyar lamari cewa an kashe ɗan jaridan a ofishin jakadancinta. Binciken da hukumomin ƙasar Saudiyya suka yi ya bayyana waɗanda keda hannu a kisan tare da nuni da cewa yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ne ya bayar da umurnin hakan a kaikaice. Sakamakon binciken da hukumar leƙen asirin ƙasar Amurka wato ClA ta yi ya bayyana ƙarara cewa yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ne keda alhakin kashe ɗan jarida Jamal Kashoggi, lamarin da ya kasance kanon Labarai a fadin duniya.

A yayinda wannan yanayin Yariman Saudiyya mai jiran gado ya kai ziyara a wasu kasashen larabawa daga bisani kuma ya halarci taron koli ƙasashen G20 da aka gudanar a Argentina. A lokacin da yake ziyartan sarakuna da shugabannin gargajiya a ƙasashen Larabawa ya yada zango a ƙasar Tunisia dake mulkin demokradiyya, a ƙasar da dinbin al'umar ƙasar suka gudanar da zanga-zangar kyamatar kisan Kashoggi. A yayinda yake Tunisia da dubun dubatan larabawa a ƙasar sun gudanar da zanga-zangar tare da dauke da alluna dake nuna cewa yariman nada hannu a a kashe ɗan jarida Jamal Kashoggi.

Bayan kammala taronsa a Tunisia ya garzaya Argentina domin halartar taron ƙolin ƙasashen G20 inda kuma ya fuskanci ƙalubalen zanga-zanga har ma ya tilastu da  zaɓan ofishin jakadancin ƙasarsa a Argentina a matsayin masauki. Kasancewar yadda wasu kungiyoyi suka gamsu da cewa yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammed Bin Salman keda alhakin kisan Kashoggi ya sanya su gabatar da ƙara a wata kotun dake ƙasar. A yayin gudanar da taron G20 da yawan shugabannin sun yi wa yariman Saudiyyan hannunka mai sanda akan ta'asar. Bin Salman wanda bai yi wata ganawa da shugabannin kasashe ba  ya fuskanci suka ƙarara daga shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. A ɗayan barayin kuwa anga shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin na daukar hoton ƙauna tare da yarima Bin Salman.

Wasu lamurkan sun sake faruwa dangane da kashe Jamal Kashoggi inda hukumar leƙen asirin Amurka wato ClA ta yi sharhi akan lamarin ga wasu sanatocin ƙasar. Bayan kammala taron da aka gudanar a bayan fage sanata Corker da sanata Graham sun shaidawa manema labarai cewa babu ko kokonto yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ne keda alhakin kashe ɗan jarida Jamal Kashoggi. Bugu da ƙari, yanke shawarar da kotun shari'a a ƙasar Turkiyya ta yi na bayar da sammacin kame wasu na kusa da yarima Bin Salman akan kisan na nuna raguwar faɗin da'irar dake nisanta Bin Salman daga kataɓariyar ta'asar.

 

Wani muhimmin abinda taron G20 ta ƙunsa kuma ita ce rikici da yaƙin kasuwanci dake tsakanin ƙasashen Amurka da China. Kasancewar yadda Amurka ta gudanar da yarjejeniyar kasuwanci marasa daidaito tsakaninta da China, ya sanya shugaba Donald Trump yunƙurin kakkaɓawa China takunkumi a maimakon daukan matakan sulhu da suka dace.  Ganin yadda hukumar Amurka ta kakkaɓawa China takunkumi ya sanya hukumomin Chinar mayar da martani akan kayyayakin kasar Amurka, lamurkan da suka jefa ƙasashen biyu cikin rikicin kasuwanci. Abin lura anan dai shi ne, kasancewar yadda kasuwancin China ke bunƙasa a halin yanzu ya zama ƙalubale ga matsayin da Amurka keda shi a fadin duniya. Musamman yadda kanfunan Amurka ke arcewa zuwa China ya ƙara hura wutar rikicin ƙasashen biyu.

 

Wannan sharhin Malam  Yazar Can ACUN ne dake cibiyar ilimin siyasa da tattalin arziki wato SETA.

 

 Labarai masu alaka