An kashe mutane 3 a wani harin bam a Iran

Mutane 3 sun rasa rayukansu yayinda wasu da dama suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai a garin Chabahar da ya hada jihohin Sistan da Balujistan na kudu maso-gabashin Iran.

Tashar Talabijin ta Kasa ta Iran ta sanar da cewa, an kai harin kan caji ofis din 'yan sanda dake titin Ribi a garin na Chabahar.

Gwamnan Sistan da Balujistan Muhammad Hadi Marashi ya ce "A safiyar Alhamis din nan ne aka kai harin kan caji ofis din 'yan sanda inda aka jikkata mutane da dama."

Marashi ya kara da cewa, an kai harin da mota makare da bama-bamai.

Tashar Talabijin ta Iran ta ce, mutane 3 sun mutu a harin.

Tag: Iran , Bam , Hari

Labarai masu alaka