Ya ja da Saudia, ya rasa mukaminsa

Daya daga cikin kusoshin fadar White House wadanda  suka yi ka-in-da-na-in wajen ganin an sanyan sunan babban mashawarcin Muhammad Bin Salman a jerin sunayen wadanda aka kakaba wa takunkumi game da batun kisan kashoggi,ya yi murabus.

Jaridar New York Times ce ta rawaito wannan labarin daga bakin wasu ingantattun majiyoyi biyu.

An sanar da cewa, Mista Fontenrose,babban mai kula da lamurran da suka jibanci Iran da kasashen Larabawa na yankin Gulf, ya yi murabus jim kadan bayan ya gana da shugabannin gwamnatin Riyad.

New York Times ta ce kawo yanzu babu cikkakiyar masaniya kan ainahin dalilin da yasa ya yi murabus,amma a kyautata zaton Saudiyya ce sila.

Fontenrose dai ya  haddasa zazzafan cece-kuce a fadar shugabancin Amurka, sabili da fafutukar da ya dinka yi na sai an kakaba wa Saudiyyawa tsauraran takunkumai,wanda a yanzu ake ganin cewa kura za ta lafa.Labarai masu alaka