Guguwar Gaja ta dakatar da lamurka a Indiya

Tsananin guguwa a kudancin kasar Indiya ta yi sanadiyar rayuka 23.

Guguwar Gaja ta dakatar da lamurka a Indiya

Tsananin guguwa a kudancin kasar Indiya ta yi sanadiyar rayuka 23.

Kafafen yada labaran kasar Indiya sun bayyana cewar hukumomin jihar Tamil Nadu sun sanar da cewa guguwar Gaja ta yi sanadiyar rushewar gidaje da dama lamarin da ya sanya yin kaurar mutane kusan dubu 82.

Shugaban jihar Tamil Nadu Edappadi K Palaniswami, ya bayyana cewar ana ci gaba da gudanar da aiyukan ceto kuma za'a bayar da tallafi ga dukkanin wadanda lamarin ya shafa.

Karfin iska mai tafiyar kilomita 110-120 ya haifar da guguwa a yankin da hakan ya sanya yankewar wutar lantarki, rashin zuwan makarantar yara da dakatar da kamun kifi.

 


Tag: Indiya , guguwa

Labarai masu alaka