Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a Zirin Gaza

Jiragen saman Isra'ila sun yi ruwan bama-bama a yankunan Zirin Gaza daban-daban inda Falasdinawa 4 suka yi Shahada, wasu 8 kuma suka jikkata.

Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a Zirin Gaza
Bidiyon ruwan bama-bamai a Zirin Gaza da Isra'ila ta yi
Bidiyon ruwan bama-bamai a Zirin Gaza da Isra'ila ta yi

Bidiyon ruwan bama-bamai a Zirin Gaza da Isra'ila ta yi

Jiragen saman Isra'ila sun yi ruwan bama-bama a yankunan Zirin Gaza daban-daban inda Falasdinawa 4 suka yi Shahada, wasu 8 kuma suka jikkata.

Kakakin Ma'aikatar Lafiya dake Gaza Ashraf Al-Kudra ya bayyana cewa, jiragen saman ısra'ila sun kai hari a arewacin Zirin Gaza da kuma gabashin garin Refah inda suka nufi wani rukunin Falasdinawa kuma 4 sun yi Shahada yayinda 8 suka jikkata.

Sanarwar da Rundunar Sojin Isra'ila ta fitar ta ce, sun kai harin ne don ramuwar gayya ga makamin roka da aka har Isra'İla daga Zirin na Gaza ba.

Sanarwar ta ce "Jiragen yakinmu na ruwan bama-bamai a Gaza." 

Ba a bayyana da wanne irin makami aka kai harin kan mota bas ba, amma an bayyana an harba makaman roka sama da tamanin daga Zirin Gaza zuwa Isra'ila.

Kungiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Isra'ila ta ce, daya daga cikin makaman rokan ya fada kan wani gida tare da jikkata Bayahude daya.

Bayan lamarin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira taro don tattauna batun da Ministan Tsaro Avigor Liberman da Shugaban Rundunar Sojin Kasar Gadi Eisenkot.Labarai masu alaka