Shugaban Houthi ya arce zuwa Saudiyya

Shugaban 'yan Shi'ar Houthi,Abdul Salam Jabr ya dafe keya tare da shekawa Saudiyya,inda ya nemi mafaka,inji ma'aikatar sadawa ta kasar Yaman.

Shugaban Houthi ya arce zuwa Saudiyya

Shugaban 'yan Shi'ar Houthi,Abdul Salam Jabr ya dafe keya tare da shekawa Saudiyya,inda ya nemi mafaka,inji ma'aikatar sadawa ta kasar Yaman.

Jabr ya juya wa Sanaa baya don guduwa zuwa Riyadh a ranar Asabar din nan, ta hanyar yin shigar burtu, saboda ba shi izinin yin bayani gaban 'yan jarida.

 Ana kyautata zaton shugaban na 'yan Houthi zai halarci wani taron manema labarai da za a shirya a ranar Lahadin nan a ofishin jakadancin Yaman da ke Riyadh. 

Kawo yanzu babu bayani da ya fito daga bakin 'yan Shi'ar Houthi,amma tashar talabijin Al Masirah wacce ke ra'ayinsu ta sanar da cewa ana gaf da nada Deifullah al-Shami a matsayin ministan sadarwa na gwamnatin Houthi.

Tun a lokcin da rikicin kasar Yaman ya barke a shekarar 2014 ya zuwa yau,karo na farko kenan da wani babban jagoran 'yan Houthi ya ari na kare don zuwa Saudiyya.Labarai masu alaka