"MBS ya tsara rushewar tattalin arzikin Iran"

Wasu daga cikin makusantan Muhammad Bin Salman sun sanar da cewa,ba Jamal Kashoggi ba Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya tsara halakawa ba, har da wasu sanannun 'yan kasar Iran.

"MBS ya tsara rushewar tattalin arzikin Iran"

Wasu daga cikin makusantan Muhammad Bin Salman (MBS) sun sanar da cewa,ba Jamal Kashoggi ba Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya tsara halakawa ba, har da wasu sanannun 'yan kasar Iran.

A cewarsu, shekaru biyu da suka gabata, wasu hamshakan attijaran Iran wadanda ke adawa da gwamnatin kasarsu sun gana da shugabannin Saudiyya,Amurka da na Hadaddiyar Daular Larabawa don tabbatar da shirinsu na rugurguje tattalin arzikin Iran da kuma halaka wasu sanannun kasar.

Jaridar New York Times ta rawaito daga wasu majiyoyi cewa,Yarima Bin Salman da makusantansa wadanda a yanzu haka duniya ta yi caa kansu sabili da kisan Kashoggi, sun dade suna shirye-shiryen kashe wadannan Iraniyawan.

Haka zalika Jaridar ta tabbatar da cewa,wani attajirin Amurka dan asalin Lubnan,Yarima mai jiran gado na Hadaddiyar Daular Larabawa,Muhammed bin Zayed Al Nahyan tare da mashawarcinsa George Nader sun shirya wata gaggarumar makarkashiya don durkusar da tatattlin arzikin Iran kwata-kwata.

A cewar majiyoyin,don cimma nasara Nader ya gana da Bin Salman da kuma shugabannin fadar White House.

Ba'isra'ile Joel Zamel,wanda ke alakar kud-da-kud da cibiyoyin tsaro da na leken asirin kasar Yahudu na a sahun wadanda suka ruwa da tsaki a wannan shirin. 

 

 Labarai masu alaka