Taron Sochi da jibge garkuwar S-300 a Siriya

A ƴan kwanakin da suka gabata, lamurka masu muhimmanci sun faru a ƙasar Siriya. Matakan da Turkiyya ta dauka a yarjejeniyar Sochi ta yi nasarar kange kai hare-haren da gwamnatin Asad wacce lran da Rasha ke goyawa baya a yankin ldlib.

1069884
Taron Sochi da jibge garkuwar S-300 a Siriya

A ƴan kwanakin da suka gabata, lamurka masu muhimmanci sun faru a ƙasar Siriya. Matakan da Turkiyya ta dauka a yarjejeniyar Sochi ta yi nasarar kange kai hare-haren da gwamnatin Asad wacce lran da Rasha ke goyawa baya a yankin ldlib. Bugu da ƙari, Turkiyya ta rataɓa hannu akan wata yarjejeniyar tsakanin Rasha da lran a Sochi. A yarjejeniyar; a yayinda aka aminta da kare yankin ldlib mai mazauna mutane miliyan uku, Turkiyya da Rasha dai sun aminta akan gudanar da ayyuka tare. A yarjejeniyar, Rasha da Turkiyya zasu kaddamar da yankin zaman lafiya mai tsawon kilomita 15-20, za'a kuma buɗe titunan m4 da m5 domin sufuri cikin sauki da zummar bunƙasa kasuwanci; haka kuma ƙasashen biyu zasu yi amfani da jiragensu marasa matuƙa domin sanya ido a yankunan ldlib. Wani muhimmin lamarin da ya afku a Siriya kuwa shi ne kakkaɓo jirgin yaƙin Rasha kirar lL-20 da Siriya ta yi bisa kuskure. A yayinda Rasha ke zargin lsra'ila akan lamarin, lsra'ila na zargin gwamnatin Asad ne da cewa ta aikata hakan bisa rashin sani. A sakamakon haka ne Rasha ta baiwa gwamnatin Asad makamin kare samaniya kirar S-300.

A Yarjejeniyar Sochi da Turkiyya ta rataɓa hannu da Rasha domin magance matsalolin ldlib, mafi yawan aiyukan tabbatar da hakan zai rataya ne akan wuyar ƙasashen biyu. Turkiyya dai na ganin cewa akwai matsaloli da ƙalubaloli akan tabbatar da yarjejeniyar. Tabbas akwai aiki ja a gaban Turkiyya fiye da sauran bangarorin, babban ƙalubalen da Turkiyya ke fuskanta a ldlib shi ne kasancewar kungiyoyin tada zaune tsaye da suke neman hakince yankin. Akwai bukatar a kauda kungiyar haɗakar Tahrir Al Sham domin tabbatar da tsabtace yankin daga miyagun makamai. Domin tabbatar da haka, ya ɗoru akan wuyar Turkiyya da ta magance dukkanin kungiyoyin dake tada fitina a cikin kasarta da kuma yankunan baki daya.

Domin tabbatar da yarjejeniyar Shoci akwai bukatar a dauki mataki akan dukkan kungiyoyin dake rike da miyagun makamai a ldlib. Da taimakon hukumomin Turkiyya an yi nasarar janye tankokin yaƙi, gurnet da rokokin yaƙi da ƴan adawar gwamnatin kasar suka jibge a ldlib. Haka kuma an dauki matakan yadda ba zasu iya kaiwa gwamnatin hari ba, inda aka kuma ɗauki matakan kauda dukkanin nau'o'in makamai da suka haɗa da makamin 23-mm da 57-mm daga yankin.

A sanadiyar yarjejeniyar Sochi da Turkiyya da Rasha suka rattaba hannu akai an yi nasarar dakatar da dukkan hare-haren da ake kaiwa ta sama a yankin, lamarin da ya ƙara samawa mutane yankin zaman lafiya, musamman a yankin arewacin Hama da kusan mutane dubu 60 da suka yi hijira daga yankin suka fara komawa gidajensu. Turkiyya ta yi nasarar kare rayuwar al'umma miliyan 3 da kuma dukiyoyinsu a yankin.

ldan muka dubi ɗayan maudu'in game da yankin kuma, kakkaɓo jirgin yaƙin ƙasar Rasha ya sanya Rashar yin kakkausar suka da zargi ga ƙasar lsra'ila, duk da dai lamarin bai haifar da rigima tsakanin ƙasashen biyu ba, ya sanya Rasha mikawa gwamnatin Asad makami kirar S-300, lamarin da zai kange lsra'ila daga yin katsalandar a sararin samaniyar Siriya. lsra'ila dai ta jima tana kaiwa ƙungiyoyin Hizbullah da dakarun lran dake Siriya hari, amma ko sau daya Rasha bata taɓa kakkaɓo jirgin yakinta ba, kasancewar yadda Siriya bata da isassun makaman kare sararin samaniyarta ya baiwa lsra'ila damar kaddamar da hare-hare a ƙasar a duk lokacin da ta buƙaci haka.

Baya ga ƙara samar da tsaron sararin samaniyar Siriya, makamin samaniyar S-300 da Rasha ta baiwa Siriyar zai taimaka mata a fannoni da dama. Bugu da kari, zai taimaka wajen ƙalubalantar rundunar da Amurka ke jagoranta da ma rundunar sojan saman Turkiyya a kasar, a takaice dai wannan makamin sararin samaniya kirar S-300 ba wai lsra'ila kawai gwamnatin Siriya zata ƙalubalanta da shi ba, har da ma sauran dukkan ƙasashen dake katsalandar a sararin samaniyar ƙasar Siriyar.Labarai masu alaka