Azzalumar gwamnatin Siriya da sojin Rasha na ci gaba da kai wa fararen hula hari

Mutane 17 ne suka jikkata sakamakon hari ta sama da dakarun gwamnatin Siriya karkashin jagorancin Bashar Al-Assad da sojin Rasha suka kai a garin Idlib da Hama na Siriyan.

Bidiyon ruwan bama-bamai da azzalumar gwamnatin Assad ke yi a Idlib

Bayanan da aka samu daga majiyoyin yankin na cewa, jiragen saman Rasha da gwamnatin Assad sun kai hari a yankunan Habit, Jerjenaz, Hish, Temenia da Hama da ke kudancin Idlib da kuma yankin Latamne na Hama.

An jikkata mutane 17 sakamakon hare-haren.

Daga cikin mutanen da aka jikkata har da wasu yara kanana 2 da suke a makarantar Jerjenaz.

Daraktan Kungiyar kara Fararen Hula a Siriya Mustafa Haj Yusuf ya ce, an kai hare-haren da safiyar Litinin din nan kuma an jikkata mutane 17.

Tag: Rasha , Assad , Hama , Idlib , Hari

Labarai masu alaka