An daure mai baiwa Trump shawara bayan kamashi da laifin yiwa kotu karya

An daure tsohon mai baiwa shugaba Donald Trump shawara akan kanfen a kasashen waje George Papadopoulos a sanadiyar shararawa kotu karya.

Kotu ta yanke mai hukuncin kwanaki 14 a gidan kaso da kuma tarar biyar kudi dala dubu 9,500.

Zai dai yi sa’o’i 200 a gidan wakafi domin bautawa kasa, ya dai kasance mai baiwa Trump shawara na farko a harkokin kanfen din 2016 da za’a fara tasa kyeyarsa zuwa kurkuku tun bayan fara binciken Robert Mueller akan bakadalar zabe.

Papadopoulos ya yi nadamar karyar da ya yi wa kotu a watan Oktoba, sai dai shugaba Trump ya nisanta kanshi daga Papadopoulos inda ya baiyawna cewar bai taba saninsa ba.Labarai masu alaka