Wata Kasa ta ba wa 'yan sanda masu teba umarnin su rage kiba ko su rasa aiyukansu

Indiya ta ba wa 'yan sandan kasar da suke da kiba da ta wuce ka'ida da su rage teba ko su rasa aiyukansu.

Wata Kasa ta ba wa 'yan sanda masu teba umarnin su rage kiba ko su rasa aiyukansu

Indiya ta ba wa 'yan sandan kasar da suke da kiba da ta wuce ka'ida da su rage teba ko su rasa aiyukansu.

Labaran da BBC ta fitar na cewa, Daraktan 'yan sandan yankin karnataka Bhaskar Rao ya bayyana cewa, akwai damuwa matuka kan yadda kiba da teba ke karuwa a tsakanin 'yan sandansu kuma a watanni 18 da suka gabata 'yan sanda sama da 100 ne suka mutu saboda cututtuka da suke dalaka da kiba mai yawa.

Rao ya ce, a yankinsu akawai 'yan sanda dubu 14, kuma suna shirin samar da wasannin tsalle-tsalle ga 'yan sanda nasu wadanda suke da kiba sosai.

Ya ce,tun watanni 6 da suka gabata aka fara aiyukan ganin 'yan sandan sun rage kiba kuma wadanda ba su yi aiki da dokar ba za su iya rasa aiyukansu gaba daya.

Ana ba wa 'yan sandan horon motsa jini kamar yadda likitoci suka bayyana wanda suka hada da ninkaya, Yoga da sauransu.

 Labarai masu alaka