Guguwa ta dauki ran wani jariri a Amurka

Wata guguwa da ta kunna kai jihar North Dakotata Amurka tare da yin sanadiyyar mutuwar wani jariri sabon haihuwa.

Guguwa ta dauki ran wani jariri a Amurka

Wata guguwa da ta kunna kai jihar North Dakotata Amurka tare da yin sanadiyyar mutuwar wani jariri sabon haihuwa.

Mahukuntan Kasar sun ce, guguwar da ta yi karfi a arewa maso yammacin jihar ta kai har ga wajen shakatawa na Prairie View Caravan wadda ta janyo rasa ran wani jariri sabon haihuwa.

An bayyana cewa, guguwar ta kuma jikkata mutane 20 daga cikin 28 da ke filin shakatawar.

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa ta ce, guguwar na gudun kilomita 170 a kowacce awa.Labarai masu alaka