Adadin mutanen da ambaliya da zaftarewar kasa suka kashe a Japan ya karu

Ya zuwa mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a Japan sun kai 195.

Adadin mutanen da ambaliya da zaftarewar kasa suka kashe a Japan ya karu

Ya zuwa mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a Japan sun kai 195.

Hukumar 'Yan sandan Japan ta bayyana cewa, daga makon da ya gabata zuwa yau an rasa yauka 195 saboda ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da aka samu.

Mahukuntan Japan sun ce,  har yanzu ana ci gaba da neman mutane 60 kuma ana fargabar adadin wadanda suka mutu na iya daduwa.

A garuruwan Hiroshima, Okayana da Ehime ma'aikata sama da dubu 70 suke aiyukan ceto.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ga Kashe Gobara ta ce, akwai kusan mutane dubu 6,70 da suke fake a wani waje.

An kuma bayar da umarnin kwashe mutane miliyan 5.9 da jihar.

Sakamakon Ibtila'in da ya faru ya sanya Firaministan Japan Shinzo Abe fasa ziyarar da ya shirya kai wa Kasashen Turai da Gabas ta Tsakiya.Labarai masu alaka