'Yan shi'ar Houthi na ruwan rokoki kan Saudiyya

Saudiyya ta yi raga-raga da wani makamin roka da aka harba daga Yaman zuwa yankinta na Jazan.

'Yan shi'ar Houthi na ruwan rokoki kan Saudiyya

Saudiyya ta yi raga-raga da wani makamin roka da aka harba daga Yaman zuwa yankinta na Jazan.

A cewar tashar talabijin Saudiyya Al Ihbariyya,jam'ian tsaron kasar Saudiyya sun tarwatsa makamin rokan da 'yan Houthi suka harba wa kasar.

A gefe daya kuma, a labarin daka bayar a yau a kafar yada labarai mallakar 'yan Houthi,an tabbatar da cewa 'yan Shi'ar sun yi ruwan rokoki kan wasu sansanin sojojin kawancen kasashen kasashen Larabawa da na gwamnatin kasar Yaman.

'Yan Houthi sun fara kai wa Saudiyya Hare-hare Rokoki lokaci zuwa lokaci,tun a ranar 26 ga watan Maris na shekarar 2016, a lokacin da sojojin kawancen kasashen Larabawa da ta ke jagoranta suka fara kaddamar da faramakai  a Yaman da zummar tallfa wa halatacciyar gwamnaitin Yawan.Labarai masu alaka