Rayuwa ta tsaya cak a New Delhi

Rayuwa ta tsaya cak a New Delhi sakamakon gurbacewar yanayi da ta durkusar da lamurra ga baki daya a babban birnin kasar Indiya.

Rayuwa ta tsaya cak a New Delhi

 Rayuwa ta tsaya cak a New Delhi sakamakon gurbacewar yanayi da ta durkusar da lamurra ga baki daya a babban birnin kasar Indiya.

Shugbannin Indiya sun yanke shawarar dakatar da gine-gine a New Delhi a tsawon kwanaki 2,saboda yadda lamarin yayi matukar tsamari.

Wannan matakin ya biyo bayanin da hukumar bin diddigi da sa ido kan matsalar gurbacewar yanayi ta India ta yi, na ayyana halin da New Delhi ta tsinci kanta a ciki, a matsayin lamari "Mafi Muni da Tayar da Hankali".

An kiyasta ninkuwar dattin iskar New Delhi da kashi 170 cikin dari.

A cewar Hukumar kiwon lafiya ta Duniya WHO, wannan sakamakon ya ninka na wanda za a iya cewa an hau tudun tsira, sau 6.

A 'yan makwannin nan,mahaukaciyar guguwa mai kunshe da kura da lodin datti na ci gaba da bibiyar yankin Arewacin Indiya,wanda hakan ya ninka yawan gurbacewar yanayi a birane da dama na kasar.

 

 Labarai masu alaka