An kashe 'yan Shi'ar Houthi 50 a Yaman

An kashe 'Yan Shi'ar Houthi na Yaman 50 a yayin wani rikici da suka fafata da dakarun kasar.

991079
An kashe 'yan Shi'ar Houthi 50 a Yaman

An kashe 'Yan Shi'ar Houthi na Yaman 50 a yayin wani rikici da suka fafata da dakarun kasar.

Rundunar sojin Yaman ta ce, sun kwace iko da yankin Al-Jah da ke lardin Hudayd.

Sanarwar da Cibiyar yada Labarai ta Dakarun Al-Umalika mai alaka da gwamnati ta fitar ta ce, a yankin Al-Jah na gundumar Baytul Fakiyya da ke lardin Hudayd ne aka samu arangama tsakanin mayakan Houthi da dakarun gwamnatin yaman.

A binciken da aka gudanar an kama makamai da kayan yaki daga hannun 'yan ta'addar.

A gefe guda kuma, a yankin kudu maso-gabashin lardin Shabwa an kashe sojoji 2 tare da jikkata wasu bayan harin kwantan bauna da aka kai musu.Labarai masu alaka