‘Yan Shi’ar Houthi sun sake kai wa Saudiyya hari

Makaman garkuwar Saudiyya sun yi raga-raga da wata rokar da ‘yan shi’ar Houthi suka harba daga Yaman zuwa birnin Nejran, na Saudiyya.

‘Yan Shi’ar Houthi sun sake kai wa Saudiyya hari

Makaman garkuwar Saudiyya sun yi raga-raga da wata rokar da ‘yan shi’ar Houthi suka harba daga Yaman zuwa birnin Nejran, na Saudiyya.

A cewar wata sanarwar da kakakin kwawancen sojojin kasa da kasa wanda Saudiyya ke jagoranta, Turki al Maliki ya yi,wacce kuma aka wallafa a  kafar yada labarai ta Saudiyya, SPA, an harba makamin roka daga garin Sada na Yaman zuwa yankin Nejran na Saudiyya da ke kan iyakar kasashen 2.

Maliki ya ce makaman garkuwar Saudiyya sun tarwatse rokar,kuma   kawo yanzu ba a samu bayani ba game da ko an akwai asarar rai ko kuma a’a , a yankin da sassan rugujajjen makamin suka fadi.

Maliki ya ce ci gaba da kai hare-hare da ‘yan Shi’ar Houthi ke yi, alama ce da ke nuna cewa Iran na ci gaba da tallafa  musu da makamai,kuma wannan hare-haren na ‘yan Houthi ya yi hannun riga da ayoyin doka na Majalisar Dinkin Duniya masu lamba 2216 da 2231, haka zalika wannnan tashin-tashin na iya jefa zaman lafiyar gabas ta tsakiya cikin mawuyacin hali.

 ‘Yan Houthi wadanda ke fafutukar hambarar da mulkin Yaman,na ci gaba da iko da a Sana’a babban birnin kasar, da kuma wasu yankuna da dama tun a shekarar 2014.A yayin da kawancen da Saudiyya ke jagornat ke ci gaba da tallafa wa halattaciyar gwamnatin Yaman.

 Labarai masu alaka