'Yan shi'ar Houthi sun kai wa Saudiyya hari da makamin roka

A ranar Alhamis 22 ga watan Maris na shekarar bana,'yan shi'ar Houthi sun kai wa kamfanin man fetur na Saudiyya "Saudi Aramco" wacce ke a kudancin kasar, hari da makamin roka.

'Yan shi'ar Houthi sun kai wa Saudiyya hari da makamin roka

A ranar 22 Alhamis na watan Maris na shekarar bana,'yan shi'ar Houthi sun kai wa kamfanin man fetur na Saudiyya "Saudi Aramco" wacce ke a yankin Najran na kudancin kasar, hari da makamin roka samfurin Badr-1.

'Yan tawayen Houthi ne sun wallafa wannan labarin a tashar talabijin Saba,inda suka ce : 

"Makamanmu na da karfin cim ma kowane makiyinmu.Wadanda suka yi wa al'umarmu kisan gilla tare da durkusar da kasar Yaman, za su dandana kudarsu".

Saudi Ramco ta yi amfani da kafar yada labarai ta Reuters don karyata batun, tare da bada tabbacin cewa dukannin kamfanoninta na hakar man fetur na lafiya kalau.

 

 

 


Tag: shi'a , houthi

Labarai masu alaka