" Turkiyya ce kawai ta ɗauki matakan da suka dace domin samar da zaman lafiya a Siriya"

Firaministan Turkiyya Binali Yıldırım ya bayyana cewar ƴan yankin Afrin dubu 350 zasu koma gidajensu idan aka kammala hare haren reshen zaitun domin kuɓutar da al'ummar yankin daga ƴan ta'addar PKK-PYD/ YPG da DEASH.

Yıldırım  a yayinda yake jawabi a taron sojojin ruwa a garin Kocaeli ya tabbatar da cewa Turkiyya na wannan harin ba wai domin kare kanta kawai ba, harma da kare al'umar yankin da dukiyoyin su da kuma kauda ƙalubalantar ta'addanci daga yankunan baki daya.

Firaministan ya ƙara da cewa bayan kammala yaƙin Firat Kalkanı a bara kusan mutun dubu 140 suka koma gidajensu.

Ya tabbatar da cewa kwashe shekaru 7 da akayi ana jidali a Siriya hakan ya farune saboda in banda Turkiyya babu wata ƙasa da ta ɗauki matakan da suka dace. A cewar sa Turkiyya ce kawai ta ɗauki matakin ƙaddamar da hare-haren Firat Kalkanı da aka kashe ƴan ta'adda dubu 3 da dari 6. A yanzu kuma tana ɗaukar matakan kare yankunan da suka yi makwabtaka da ita ta yamma domin kuɓutar da Türkmen, Larabawa da Kurdawan yankin dubu 500 daga uqubar ta'addanci.

Yıldırım ya ƙara da cewa bisa ga nasarorin da aka samu kawo yanzu da yardar Allah za'a share yankin daga ƴan ta'addar PKK-PYD/ YPG da DEASH daga bisani kuma al'umar yankin zasu koma gidajensu su ci gaba da rayuwar su cikin lumana.Labarai masu alaka