"Ba za mu halarci taron sulhun da Rasha ta shirya ba, don ta na kashe fararen hula a Siriya"

Shugaban kungiyar adawa da gwamnatin Siriya Ahmet Tuna ya bayyana cewar kisar farar hula da rataya tutar Siriya da Rasha ke yi ne dalilan kin halartar taron samar da zaman lafiya a Siriya da ake gudanar wa a birnin Sochi dake kasar Rasha.

900248

Shugaban 'yan adawar ya nuna rashin amincewarsa ga yadda aka sanya tutar gwamnatin Asad a filin taron lumanar gabanin dawowar sa a Ankara babban birnin Turkiyya.

Haka kuma Tuma, wanda tsohon shugaban 'yan adawa ne wanda ke wakiltar sojoji masu adawa da Asad ya bayyana cewa sun fasa halartar taron Astana ne saboda Rasha ta karya alkawarin da ta dauka. A cewar sa:

"Rasha ta kasa cika alkawarin da ta dauka, ba ta bar kashe farar hula ba, kuma ba ta daina rataya tutar gwamntin Asad ba a tarukanta. Saboda haka Rasha na da gurguwar diflomasiyya" 

Saboda wadannan dalilan, Tuma ya bayyana cewa sun yanke shawarar kada su shiga cikin majalisa, Inda ya kara da cewa:

"Kungiyar Turkiyya za ta ci gaba da faɗar bukatunmu." 

Ana dai ci gaba da gudanar da taron sulhun Siriya amma a bayan labule, ana tunanen za'a bayyana abubuwan da za'a tattauna a taron bayan an kammala shi.

 Labarai masu alaka