Dakarun Saudiyya sun kashe 'yan ta'addar Houthi 11 a Yaman

Dakarun Kawancen Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun kai hari ta sama a Sana babban birnin kasar Yaman inda suka kashe 'yan ta'addar Houthi 'yan shi'a 11.

An bayyana cewa, an jikkata mutane da dama a harin inda aka kuma fasa tankokin mai 2 tare da lalata wata ma'ajiyar makamai.

A gefe guda kuma 'yan ta'addar Houthi sun tayar da bam a gidan shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta Rakip da ke yankin Beran a gundumar Nahm.

Kungiyar rakip dai ta dade tana bayar da rahotanni game da aiyukan keta hakkokin dan adam da Houthi ke yi a Irhab.

Tsawon lokaci ana yakin basa sa a Yaman inda 'yan tawayen Houthi suke fafata wa da dakarun Saudiyya da ke goyon bayan gwamnatin Abdurrab Hadi mansur.Labarai masu alaka