'Yan ta'ddar Shi'ar Houthi sun kashe sojoji 7 a yayin da suke Sallar Idi a Yaman

Sojoji 7 ne suka mutu sakamakon harin bam da aka kai a lokacin da ake Sallar Idi a gabashin lardin Ma'ariba na kasar Yaman.

'Yan ta'ddar Shi'ar Houthi ne suka kai harin kan sojojin Yaman a lokacin da suke Sallar Idi a Masallacin gundumar Sarvah ta lardin Ma'arib. An kuma jikkata wasu karin sojoji 11 a hain.

'Yan Shi'ar na Houthi ne ke rike da iko da Sarvah wanda yanki ne mai muhimmanci game da tsaon binin Sana.

Tun bayan yunkurin juyin mulkin watan Satumban 2014 'yan Shi'ar Houthi suke rike da wasu yankunan kasar Yaman.

A watan maris din shekarar 2015 kuma Saudiyya ta jagoranci kasashen Larabawa inda suka fara kai hari kan 'yan ta'addar a Yaman.

Tag: Yaman , Shi'a , Houthi

Labarai masu alaka