Koriya ta Arewa: Za mu gama da Amurka matukar ba ta daina shigar mana hanci ba

Gwamnatin Koriya ta Arewa ta bayyana cewa, idan har Amurka ta kuskure ta yi yunkurin ganin an kifar da gwamnatin kasar to za ta kai mata hari da makaman Nukiliya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Koriya ta Arewa KCNA ya sanar da cewa, a yayin wani taro da aka gudanar a makon da ya gabata shugaban Hukumar Leken Asiri ta Amurka Mike Pompeo ya bayyanawa duniya yiwuwar kawo batun neman sauya gwamnati a Koriya ta Arewa da ke sarrafa makamashin Nukiliya don samar da makamai wanda hakan kumanya sanya Koriyan mayar da martani.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta fitar ta ce, idan har Amurka ta yi wani yunkuri na kifar da gwamnatin Koriya to za su yi luguden wuta da makaman Nukiliya kan Amurka.

Sanarwar ta ce, kalaman Pompeo sun wuce gona da iri saboda ya nuna manufar gwamnatin Trump ita ce sauya gwamnatin Koriya ta Arewa.

A yayin wani taron kan sha'anin tsaro da aka gudanar a jihar Colorado ta Amurka, shugaban Hukumar CIA Pompeo ya ce, daya daga cikin manufofin Amurka shi ne raba kasashe da niyyar sarrafa Nukiliya.Labarai masu alaka