Gobara ta yi kisa a Sin

Mutane 22 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta barke a wani gida dake jahar Ciangsu a kasar Sin

Gobara ta yi kisa a Sin

Mutane 22 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta barke a wani gida dake jahar Ciangsu a kasar Sin

Rahoton da aka karbo daga gidan talabijan din kasar CCTV ya nuna cewa gobarar ta tashi a wani bene mai  hawa biyu da ke kauyen Yushan a jahar Ciangsu.

Mutane 3 ne suka jikkata sakamakon al’amarin.

Dakarun gwamnati sun bayyana cewa an kashe wutar a take inda aka kai wadanda suka jikkata asibiti.

Ana nan ana cigaba da bincike game dalilin da ya sa gobarar ta tashi.Labarai masu alaka