Mummunar guguwa ta kashe mutane 2 a Amurka

Mutane 2 ne suka mutu sakamakon mummunar guguwa da ta afku a jihohin Oklahoma da Winsconsin na Amurka.

Mummunar guguwa ta kashe mutane 2 a Amurka

Mutane 2 ne suka mutu sakamakon mummunar guguwa da ta afku a jihohin Oklahoma da Winsconsin na Amurka.

Sanarwar da aka fitar daga hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta bayyana cewa, wani mutum a yankin Chetek na jihar Winsconsin ya rasa rransa.

An bayyana cewa, guguwar ta kuma jikkata wasu mtanen 25 amma an ce suna cikin hali mai kyau.

A garin Elk City na jihar Oklahoma kuma wwani mutum ya sake mutuwa sakamakon guguwar.

Jami'in 'yan kwana-kwana Danny Ringer ya ce, mutum 1 ya mutu inda gidaje 40 suka samu matsala wasu 70 kuma suka rushe baki daya.

 Labarai masu alaka