Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hürriyat na cewa, a ranar 16 zuwa 17 ga watan Mayu shugaba Erdoğan zai ziyarci Amurka inda yanku haka akwai matsala tsakanin kasashen biyu bayan Amurka ta amince da cewa ta bawa reshen kungiyar ta’addan PKK wanda ake kira YPG taimakon makamai. Shugaba Erdoğan yana shirya takardun da zai kai Amurka bayan dakarun Turkiyya sun yi bicike mai zurfi. Cikin takardun hada sanfarin makaman kirar Amurka, Jamus da Ingila wanda aka bawa ‘yan PKK. Haka zalika Erdoğan yana da shedar yanda aka shigo da makamen cikin Turkiyya.

Babban labarin Haber Türk na cewa, a yau ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai tafi China inda zai halarci taron Ayyukan Hadin Gwiwar Kasashen Waje sannan ya gana da shugaban kasar China Xi Jinping. A ranar 14 ga wata za a yi babban taron a birnin Bejin inda Erdoğan zai gana da dakarun kasar China a ranar 15 ga wata.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, ministan tsaron Turkiyya Fikri Işık ya bayyana cewa an yi gwajin makami mai linzami a birnin Sinop inda wannan shi ne karo na farko da Turkiyya ta yi irin wannan gwajin. A birnin Sinop aka harba makamin inda ya sauka a tekun Bahar Rum. An bayyana cewa makamin ya yi gudun kilomita 280 kafin ya fado.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, yayinda ya yi magana a taron taimakon Somaliya da MDD ta shirya ne Firaminista Binali Yildirim ya ce “ya kamata a shirya sojoji masu karfi domin yakin ‘yan Al-shabab. A watan Satumba mai zuwa ne kungiyar Horon Sojoji Ta Anadolu za ta fara horo da ilimantar da sojojin Somaliya.

Babban labarin Yeni Şafak na cewa, kasashe da dama karkashin kungiyar Hadin Gwiwar Ayyukan Yankunan Tekun Black Sea sun hadu a Istanbul. A taron ne dai aka tattauna kan saukaka ayyukan kasashen yankin inda aka yanke shawarar fara ayyukan cikin kankanin lokaci.  Labarai masu alaka