Kungiyar ta'adda ta Daesh ta zubar da jini a Iraki

Kungiyar ta'adda ta Daesh ta kai hari a Baghdad babban birnin kasar Iraki ta kashe fararen hula 24 tare da jami'an tsaro 12.

Kungiyar ta'adda ta Daesh ta zubar da jini a Iraki

Kungiyar ta'ddan ta kai harin kunar bakin wake ne a wani kantin sayayya a unguwar Sadr inda 'yan Shi'a ke zama, inda suka kashe fararen hula 24 tare da jikkata wasu 60.

Shugaban kungiyar Es-Sadr da ke unguwar Sadr, ya bukaci da a dauki matakin da ya kamata da wuri kafin kungiyar Daesh ta ci gaba da kashe mutane.

Bayan haka kuma, kungiyar ta'adda ta Daesh ta kai hari a yankin Abu Gureyb inda suka kashe sojoji da 'yan sanda 12.

An bayyana cewa jami'an tsaro sun yi kokarin kama shugaban kungiyar a yankin tare da rufe gidansa.
Labarai masu alaka