Jirgi maisaukar ungulu ya yi hatsari a Nicaragua

Mutane 3 ne suka mutu inda aka nemi tsohonshugaban kasar Nicaragua Antonio Lacayo aka rasa sakamakon fadowar wani jirgin sama mai saukar ungulu.

Jirgi maisaukar ungulu ya yi hatsari a Nicaragua

Jirgin saman ya tashi ne daga garin San Carlos zuwa Managua babban birnin kasar, inda daga cikin wadanda suka mutu har da wani dan kasar Amirka.

Rahotanni sun ce, ana zargin jirgin ya fado ne sakamakon yawaitar hazo da ake da shi a yankin.

Kakakin gwamnatin kasar Rosario Murillo ya ce, gwamnati na bakin ciki sosai game da faruwar hatsarin.

Lacayo ya shugabanci kasar a tsakanin shekarar 1990 zuwa 1997.

 


Tag:

Labarai masu alaka