Wani jirgi mai saukar ungulu ya fado a Amurka

Sojoji 11 wadanda 7 daga cikinsu na ruwa ne suka bace sakamakon fadowar wani jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Florida ta Amurka.

Wani jirgi mai saukar ungulu ya fado a Amurka

An gano buraguzan jirgin wanda ke sintirin koyawa dalibai tuki a kusa da sansanin sojin saman Eglin dake arewa maso-yammacin Florida.

Har yanzu dai ma'aikatan ceto ba su iya gano inda jikkunan mutanen dake cikin jirgin su 11 suke ba.

An sanar da cewa mutanen dake cikin jirgin su 11 ne, inda 7 daga cikinsu sojin ruwa ne.


Tag:

Labarai masu alaka