An yanke wa wani tsohon ministan Bangladesh hukuncin kisa

Kotu a Bangladesh ta yanke wa wani tsohon minista a kasar Muhammad Kayser hukuncin kisa, sakamakon samunsa da laifukan yaki, lokacin rikicin kwatar 'yanci a shekarar 1971.

An yanke wa wani tsohon ministan Bangladesh hukuncin kisa

Kotun shari'a a kasar game da yakin da aka yi a lokacin neman 'yancin kai ta tuhumi tsohon ministan mai shekaru 73 da laifuka 16 inda ta same shi da aikata 14.

Ministan ya musanta laifin da aka tuhume shi na hada kai da wasu sojin Pakistan su kai hari kan wasu kauyuka.

Lauyoyin Kayser dai sun ce za su daukaka kara.


Tag:

Labarai masu alaka