Iran ta yankewa wata mata hukuncin kisa

Kotun Iran ta yankewa wata mata hukuncin kisa sakamakon tuhumarta da aka yi da kashe wani mutun da aka zarga cewa ya yi mata fyade.

Iran ta yankewa wata mata hukuncin kisa

 

Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa dai sun la’anci wannan yanke hukuncin.

Ministan shari’a na Iran Mostafa Pour-Mohammadi ya ce, a farkon watan Oktoba ne kotu ta so ta ragawa Jabbari amma kotu ta kasa shawo kan iyalan marigayin kuma adadin da dokar kasar ta tanada a shekarar 1979 bayan juyin juya halin kasar na a zartarwa da mutum hukunci ya kare.

Amurka da Tarayyar Turai sun soki hukuncin da kuma gwamnatin Rouhani wadda ta yi yakin neman zabe da cewa za ta girmama 'yancin dan adam.

An yanke wa Jabbari hukuncin kisa ne dai-dai da dokar Alqur’ani ta ‘’qisas’’ bayanda aka same ta da laifin soke wani mutum har lahira shekarar 2007. An tsare ta a gidan yari ne yayinda kotu ke ci gaba da tuhumarta.

Shugaba Ruhani Ayatollah Ali Khamenei ne zai iya sanya baki don saukaka hukuncin, amma bai yi hakan ba.

Jama’a da dama dai sun zargi gwamnati kan yanke hukuncin kisa din amma an samu shaidu da suka tabbatar cewa ta yi yunkurin kisa har da ma sayann wuka don aikata kisan.


Reuters


Tag:

Labarai masu alaka