Hatsarin jirgi mai saukar ungulu a kasar Switzerland

Mutanen kasar Switzerland 5 ne suka rasa rayukansu sakamakon fadowar jirgi mai saukar ungulu da suke ciki a kasar.

Hatsarin jirgi mai saukar ungulu a kasar Switzerland

A yau ne  wani jirgin mai saukar ungulu ya fado a gabashin kasar Switzerland Montbeliard inda mutanen kasar 5 suka mutu.

JIrgin samfurin  EC 130 ya tashi daga tashar Lausanne  ne  yayinda zai sauka a garin  Montbeliard  ne aka samu wani kuskure.

Akalla dai mutun daya ne ya jikkata inji wani ma'aikaci a Doubs.

Reuters


Tag:

Labarai masu alaka