TRTVOTWORLD

 

TRTVOTWORLD.COM

Wannan shafin na TRTVOTWORLD.COM shafin yanar gizon Sashen Yada Labarai Ga Kasashen Waje na Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin na Turkiyya TRT ne. Wannan shafi na yada labarai da shirye-shirye a yaruka 41 na duniya kuma yana kan gaba wajen işar ga manufofin Turkiyya na cikin gida da na kasa da kasa ga kasashen duniya.

Shafin TRTVOTWORLD.COM ya mayar da hankali wajen yada shirye-shirye a shafukan yanar gizo ganin yadda duniya ta sauya da yadda ake neman labarai ta yanar gizo, baya ga amfani da mitocin gajeren zango. Yana gabatar da labarai da suka dace da kasa da kasa suke da inganci. Ana bayar da labarai da suka shafi Turkiyya, Shiyyoyi da Duniya baki daya. Labaran sukan shafi Siyasa, Raya Al’adu, Tattalin Arziki, Siyasa, Kimiyya da Fasaha. Ana gudanar da bincike, bayan samun sakamako sai a fitar da labarai. Ana bibiyar kamfanonin dillancin labarai na Turkiyya da ma na duniya don samo ingantattun labarai tare da yada su ta hanya ingantacciya.

Shafin yanar gizon TRTVOTWORLD.COM na kan gaba a duniya a tsakanin shafukan da ke bayar da labarai masu inganci kuma na gaskiya.