Tarihin TRT

TARIHI

An kafa Hukumar Gidan Rediyo da Talabijin ta Turkiyya TRT a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1964 da manufar yada shirye-shirye a madadin Kasar Turkiyya. Kuma an kafa ta karkashin dokokin kasar a matsayin mai zaman kanta. A yayin gyaran kundin tsarin mulki na shekarar 1972 sai aka mayar da ita Hukumar ta kasa wadda ba za ta dinga daukar bangare ba. Ma’ana za ta ba wa kowanne dan kasa dama.

A shekarar 1984 ne aka sake yin kwaskwarima ga dokar da ta kafa Hukumar bayan zuwan sabuwar gwamnati a shekarar 1982. Bayan an fara yada labarai ta tauraron dan adam tare da zuwan kafafen yada labarai masu zaman kansu bayan shekarun 1986, sai aka janye takaitawar yada labaran da TRT ke yi har zuwa shekarar 1990.

Bayan an gyara sashe na 133 na kundin tsarin mulki a shekarar a shekarar 1993 sai aka kyale yada labarai  na bangaren masu zaman kansu, wanda hakan ya sanya aka sake fasalin TRT. A yau TRT na yada labarai ta Rediyo da Talabijin a matsayin tashar da ba ta nuna bangaranci ko son kai a tsakanin al’umar kasar.

Kafin a kafa TRT ana amfani da kamfanin Turk Wireless wajen yada labaran rediyo, wanda a shekarar 1964 aka hade su karkashin TRT. Bayan da Rediyon Istanbul ta fara aiki a shekarar 1927, a shekarar 1928 kuma Rediyon Ankara ta fara aiki. A ranar 8 ga watan Satumban 1936ne aka ba wa ptt alhakin kulawa da gidajen rediyon. Bayan an ba wa ptt sai a ranar 28 ga watan Oktoban shekarar 1938 aka kaddamar da Rediyon Ankara a hukumance. A watan Oktoban 1938 rediyon Istanbul ta dan yi hutu wajen yada shirye-shirye, sai a ranar 19 ga watan nuwamban 1949 ta dawo bakin aiki. A lokacin da aka fara yakin duniya na 2 a shekarar 1949 ne aka mayar da su karkashin Hukumar Yada labarai da Hulda da ‘Yan Jaridu. A shekarar 1950 kuma Rediyon Izmir ta fara aiki. Bayan shekarar 1953 ita ma ta koma karkashin wannan Hukuma ta Yada labarai da Hulda da ‘Yan Jaridu.

Bayan shekarar 1960 an kafa gidajen rediyo a larduna 8 na Turkiyya. Ta hanyar aiki da dokar kundin tsarin mulki da ta kafa gidajen rediyo a matsayin masu adalci tsakanin ‘yan kasa a hekarar 1961, sai aka dauki matakin fadada karfin TRT a shekarar 1964 yadda za ta rika isa ga jama’a sosai. A shekarar 1974 anhade tashohin TRT na yankuna da na helkwata inda aka samar da TRT-1, TRT-2 da TRT-3.

A ranar 31 ga watan Janairun 1968 ne aka fara yada shirye-shiryen Rediyo a TRT. Inda Mahmut Tali ya yi jawabin farko a dakin watsa shirye-shirye na Mithatpaşa. An fara shiri na gwaci na awanni 3 a kwanaki 3 na kowanne mako. Bayan shekara 1 kuma sai aka mayar da shi kwanaki 4 a kowanne mako. Bayan kafa talabijin din Izmir a shekarar 1970 a shekarar 1971 aka kafa na Istanbul.

An nuna yadda ‘yan sama jannati suka tafi duniyar wata a shekarar 1969 da kuma bikin waka da Zeki Muren ya gabatar a akwatunan talabikin din TRT. A shekarar 1973 kuma an  kawo taron jana’izarshugaban kasar Turkiyya na 2 Ismet Inonu. Dukkan nahiyar turai da Turkiyya sun dinga samun labarin yunkurin eman zaman lafiyar tsibirin Cyprus da aka fara a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 1974. A shekarar 1975 TRT ta shirya bikin wakoki na Eurovision. A shekarar 1978 aka fara amfani da na’Urorin daukar hoto a karkashin teku, inda aka dauki wani fim mai suna “Tarihin Karkashin Teku”.  A shekarar 1979 aka fara gabatar da shirin ranar yara ta duniya ta 23 ga watan Afrilu inda yara kanana 133, da shugabanni 31 daga kasashe 5 suka halarta.

A shekarar 1974 aka fara gabatar da shirin talabijin a kowacce rana ta mako. Kuma kaso 55 cikin 100 na Turkawaa wato mutane miliyan 19 na kallon talabijin. Kuma karfin yada shirye-shiryen na iya zuwa har nisan kilomita 210.861. Alkaluman PTT sun nuna cewa, alokacinda TRT ta cika shekaru 10 da kafuwa an samuakwatunan talabijin miliyan 2 a gidajen Turkawa. A shekarar 1982 aka kafa cibiyar Eurovision wadda ta bayar da damar hada shirye-shirye a ciki da wajen Turkiyya.A ranar 31 ga watan Disamabn 1981 aka fara yada shiri da kala a akwatunan talabijin inda a 1984 wannan tsari ya gama kankama.

 

A shekarar 1986 tashar TRT ta biyu wato TRT-2 ta fara yada shirye-shşryenta da Maraba. Ashekarar 1987 tashoshin TRT-1 da TRT-2 suka fara yada shirye-shiryen ta kan tauraron dan adam na “Intelsat” wanda na haya ne. A shekarar 1989 TRT-3 ta fara aiki tare da tashar GAP-TV wanda hakan ya kawo tashoshin TRT auka zama 4. A shekarar 1990 TRT 4 ta fara aiki wadda tasha ce da aka ware don Turkawa da ke kwadago a nahiyar Turai. Ana kiranta TRT INT. A shekarar 1993 kuma aka kafa tashar TRT Avrasya don kasashen Kafkas da tsakiyar Asiya, inda a shekarar 1995 kuma tashar TV ta Majalisar Dokoki ta fara aiki.

A shekarar 1998 ne aka fara bude ofishin TRT a kasar waje wato ofishin Jamus a birnin Berlin. Tare dahakan a shekarar 1999 aka bude ofishin Akşabat a Turkmenistan, a shekarar 2000 aka bude na Baku a Azaerbaijan, na Masar a Alkahira, na Beljiyom a Brussels, inda a shekarar 2002 kuma aka bude ofishin AMurka a birnin Washigton sai a shekarar 2004 da aka bude ofishin TRT a taşkent babban birnin kasar Ozbekistan.

A shekarar 1999 ne aka kafa Cibiyar Yanar gizo ta TRT da ake kira TRT-SAYTEK inda ta samar da shafin yanar giz ona www.trt.net.tr kuma aka fara yada shirye-shirye a cikinsa.

Shekarar 2003 ta zama shekara da ba za a taba manta wa da iya a TRT da ma Turkiyya gaba daya ba. A shekarar ne TRT ta yi nasara a gasar Eurovision inda Sertap ERENER ya samu nasara bayan ya yi sharhi kan wakar “Every Way That I Can” .

A shekarar 2004 tasharmu takara bunkasa a kasashen waje inda ta zama mamba a kungiyar yada labarai ta kasashen Asia-Pacific.   

A ranar 1 ga watan nuwamban 2008 ne aka kafa tashar TRT Children wadda ita ce ta farko a kasar.a ranar 1 ga watan janairun 2009 kuma tashar TRT Kurdish wato TRT 6 ta fara yada shirye-shirye a harshen Kurdanci da lahjoji daban-daban. Sai a shekarar 2015 ne sunan tashar ya koma TRT Kurdi.

A ranar 20 ga watan Nuwamban 2008 ne aka samar da www.trtvot.world.com inda aka fara shiri a yaruka 31 na kasashen waje a yanar gizoninda ta samu matsayi na 5 a tsakanin tashoshin da ke yada shiri irin haka. A yanzu tana yada shirye-shirye a yaruka 41 zuwa ga sassan duniya daban-daban.

Tun daga kasashen Balkan zuwa tsakiyar Asiya, gabas ta tsakiya zuwa Caucasia, tashar TRT Avaz na magana da kusan mutane miliyan 250 a kasashe 27 da Jamhuriyoyi 13. A ranar 21 ga watan maris din 2009 ne TRT AVAZ ta fara yada shiri a yaren Turkanci da ake a kasashen Azabaijan, kazakstan, Kırgıstan, Ozbekistan da Turkmenistan. Tashar ta zama ta hadin gwiwar yada shirye-shirye a wadannan yaruka.

 

A ranar 8 ga watan Mayun 2009 ne tashar TRT Turk ta fara aiki wadda tashar talabijn ce da ke yada zallan al’adun Turkiyya da Turkawa.  A wannan shekara ne tashar TRT Anadolu ta fara gwajin yada shirye-shirye.Kuma an mata kallon tashar da ta hade tashohin yanki da na hwalkwatar TRT a guri guda. A shekarar 2012 ne aka mayar da TRT Anadolu ta koma TRT Diyanet wadda ta kuma ci gaba da yada shirinta awanni 24 kowacce rana da dare. A ranar 16 ga watan nuwamban 2009 ne tashar TRT Music ta fara aiki, wadda ta ke kawo wake-waken yturkawa da m ana kasashen waje.


TRT ta haga gwaiwa da tashar Eronews ta nahiyar Turai, wanda hakan ya sanya a watan janairun shekarar 2010 Euronews ta saka Turkanci a matsayin yâre da za ta dinga yada shirye-shirye da shi.

A ranar 18 ga watan Maris din 2010 TRT haber ta fara aiki. A ranar 4 ga watan Afrilun shekarar 2010 kuma tashar TRT Al-Turkiyye ta fara aiki wadda ta ke yada shirye-shirye don kasashen Larabawa. A shekarar 2015 ne aka canja sunan tashar zuwa TRT Al-Arabiyya.

Tasarin cigaban yada shirye-shirye na fasahar HD na TRT ya mayar da hankali kan harkokin wasanni da shirye-shiryen gaskiya.

A watan Agustan 2010 tashar TRT Spor ta fara aiki, tashar ta talabijin an kawo wasannin kasa da na kasa da kasa ga masu kallo.

A watan Janairun 2011 kuma tashar TRT School ta fara aiki wadda tashar talabijşn ce da ke kawo shirin ga dukunnan rukunin al’uma don iilamnatarwa da yada al’adu.

A yau TRt na da tashoshi 14na talabijin. 5 na kasa, 5 na yankuna, gidajen rediyo 3 na kasa da kasa da 3 na cikin gida da suka kunshishi yaruka 41 da ake yada su ta adireshin yanar giz ona trt.net.tr da kuma www.trtvotworld.com.

Akwai kuma mujallu na TRT Children da Television da kuma Radiovision da ak bugawa a madadin Hukumar TRT.