Talabijin din TRT

Talabijin

Akwai tashohin talabijin na kasa, shiyya da ma kasa da kasa. Tashar TRT da ke ba wa Turkiyya da dukkan duniya labarai masu inganci, tana isa zuwa wajen yankunan Anadolu da kaso 99 cikin 100 tare da bayar da labaran raya al’adu, wasanni, zamantakewa, Suna kuma gabatar da shirye-shirye da suka dace da kowa da kowa. Baba da yaro, mata da maza.

Manufar yada shirye-shiryen TRT shi ne, ilmantarwa, raya al’adu, koyar da sana’a ga dukkan bangarori na al’uma ba babba ba yaro, ta hanya mai kyau ba tare da nuna bangaranci ba tana bayar da labarai da dumu-duminsu tare da bayar da gudunmowa wajen raya al’adu da ailmantarwa, tana nishadantarwa tare da hade kan al’umar kasa ta hanya mafi kyau.

TRT 1

TRT-1 Tashar iyali. Tashar TRT 1 ce tashar da aka fi kalla a Turkiyya. Tana mayar da hankali wajen ilamnatarwa, raya al’adu, wasan kwaikwayo, wake-wake, nishadantarwa, wasanni da labarai. Tana kuma sadarwa ga dukkan sassan Turkiyya. Kaso 99 cikin 100 na TRT-1 na isa ga dukkan duniya ta yanar gizo da tauraron dan adam.

TRT WORLD

TRT WORLD Tasha ce da ke gabatar da komai nata a cikin yaren Turanci. Tana zuwa ga kowanne sashe na duniya. Tashar talabijin ta TRT World na gabatar da labarai da suka shafi rayuwar bil’adama a yau.
TRT HABER

TRT- HABER Tashar na gabatar da labarai sababbi fil. Labaran da suka shafi siyasa, nazari, muhawara, wasanni, labarun gaskiya da na sana’o’i ne suka kasance numfashin TRT Haber. Tashar na gabar da duk wasu shirye-shirye da suka shafi rayuwar yau da kullum. Ba ta kwai sai da zakara. Ku ma ku yi amfani da ita ta yadda ya kamata. Labaran tashar TRT Haber n ana a ko’ina..

TRT SPOR

TRT SPOR Tashar TRT Spor ta fara yada shirye-shirye a shekarar 2010. Tana kawo duk wasu wasanni da suka shafi Turkiyya da m ana sauran aksashen duniya. Tana kawo gasar kasa da ake buga wa a ko’ina. Tana kawo wasanni kai tsaye sannan ta ba wa kowanne bangare na wasa muhimmanci.

TRT AVAZ

TRT-AVAZ Tashar TRt Avaz ta fara aiki a watan maris din 2009. Tana kuma yada shirye-shiryenta don kasashen Ozbekistan, Kazakistan, Kırgızistan, TUrkmenistan, Azerbaijan, Bosniya, Albaniya da ma Turkiyya, tana yada shiri a yarukan wadannan kasashe. Tashar ta mayar da hankali wajen yin shirye-shirye don Turkawan da ke rayuwa a gabas mai nisa da kasashen Balkan.Tana samar da hadin kai a bangaren yare tsakanin Turkiyya da sauran kasashe. A lahjojin Turkanci da dama Avaz na nufin murya. Tashar TRT Avaz ta zama muryar kasashen da ke magana da yaren Turkanci, tun daga gabas ta tsakiya zuwa caucasia, tashar TRT Avaz na magana da kusan mutane miliyan 250 a kasashe 27 da Jamhuriyoyi 13..

TRT ÇOCUK

TRT Yara Tashar TRT Yara na samar da wakoki, fina-finai, labarai da hikayoyidon yara kanana. Manufarta shi ne Tarbiyyar yara masu taso wa su zama masu albarka da alfanu ga kasashensu da al’umunsu.Tana bayar da ilimi da ya dace da tsarin duniya tare da taimaka wa wajen ilmantar da yara kanana da ba su tarbiyya tagari. Tana tallata al’adun da yaren Turkiyya sosai kuma ta hanya mai kyau. Tana da manufar ilmantarwa tare da nishadantar da yara kanana.

TRT BELGESEL

TRT Labarun Gaskiya Tashar TRT Labaran Gaskiya na gabatar da shirye-shiryenta a yarukan Turanci, Jamusanci, Faransanci, Rashanci da Turkanci wato yaruka 5 kenan. Tana gabatar da shirye-shirye na gaskiya da yadda lamurra suke a bangaren zamantakewa, rayuwa, namun daji, wasanni, sana’o’i, kimiyya da fasaha. Tashar ta fara aiki a ranar 17 ga watan oktoban shekarar 2009.

TRT MÜZİK

TRT WAKE-WAKE Wannan tasha ta TRT wake-wake tana gabatar da wakokin Turkiyya da na duniya, tana shirya gasa, tana gabatar da labaran gaskiya, tana shirya bukuwan cashiya tare da gabatar da su kai tsaye. Ta fara aiki a ranar 16 ga watan Nuwamban 2009 kuma tana gabatar da wakokin Turkiyya da na sauran kasashen duniya ga masu kallo.

TRT ARAPÇA

TRT AL-ARABIYYA Wannan tasha ta kafu ne da manufar karfafa alakar Turkiyya da kasashen yankunanta. Tashar ta zama muryar hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da duniyar Larabawa. Ta zama talabijin din Yurkiyya da kasashen Larabawa. Kowane bangare na al’uma zai iya kallon tashar. Tana gabatar da labaran siyasa, wasanni, raya al’adu, sana’o’i, tarbiyya da nishadantarwa. Tashar talabijin din ta fara aiki a watan Afrilun 2010. Tashar na masu kallo miliyan 350 a kasashen Larabawa 22 inda ta ke kara karfin alakarsu da Turkiyya.

TRT TÜRK

TRT TURK Tashar ta fi gabatar da shirye-shiryenta a yaren Turkanci. Kuma tana tallata Turkiyya ta cikin shirye-shiryenta na ailmantarwa, sana’o’i da raya al’adu. Tana bayar da taimako ga al’umunmu da suke kasashen waje waje kara kulla alaka da dankon zumunci tare da share musu hawayensu ko ma a wanne bangare na duniya suke.

TRT KURDÎ

TRT KURDI Wannan tasha na gabatar da shirye-shirye ga kasa da kasa a yaren Kurdanci musamman ma ga kasashen da ke kusa da Turkiyya. Tana kara karfafa dangantakar turkiyya da wadannan kasashe. Tashar da ke kara hada kan al’umarmu waje guda kuma iyalai suke kallonta sosai ta fara aiki ne a watan Janairun 2009.

TRT OKUL

TRT MAKARANTA Wannan tasha ta TRT Makaranta ta fara aiki a watan janairun 2011. Ana gabatar da shirye-shiryenta bisa tsarin manhajar da jami’ar Anadolu ta samar wa dalibai. Haka zalika TRT na samar da tsare-tsare da dama na shirye-shiryen da ake yi da suka shafi wasanni, raya al’adu, ilmantarwa, nishadantarwa da bayar da tarbiyya.

TRT 3

TRT 3 Wannan tasha ta TRT 3 na yada abubwuan da suke afkuwa a zauren Majalisar Dokokin Turkiyya Mai Girma. Tashar TRT 3 na kuma yada shirye-shiryen TRT Sport wato tashar wasanni.