Rediyon TRT

Rediyo


Ana ganin kamar mun ci baya a bangaren kimiyya da fasaha, to amma a bangaren sadarwar rediyo abin ba haka ya ke ba. Domin a ranar 6 ga watan Mayun 1927 a lokacin da kusan kowanne bangare na duniya ya fara amfani da rediyo, al’umar turkawa ma sun fara amfani da ita. A ranar 1 ga watan Mayun 1964 aka samu babban cigaba bayan an kafa Hukumar gidan rediyo da Talabijin ta Turkiyya TRT. A yau akwai tashphin radiyo na kasa guda 5, akwai na yankuna5, na cikin gida 3 da kuma na kasa da kasa 5. Kuma suna yada shirye-shirye cikin adalci da ba wa kowanne bangare na al’uma dama baidaya a bangarorin labarai, yada al’adu, kade-kade, ilmantarwa, nishadantar ta cikin yaren Turkanci mai inganci.

TRT RADYO 1

TRT Rediyo 1 Wannan tasha nam ayar da hankali wajen yada shirye-shirye a bangaren ilimi, labarai, raya al’adu da kuma bangaren kimiyya da fasaha ga duk wanda ya ke son ilmantuwa a wannan fanni. Tana bayar da ilimi na gaskiya ba tare da nuna bangaranci ba. Tun shekarar 1927 tashar TRTRediyo 1 take yada yada shirye-shiryenta. Tashar ta yadu ako’ina.

TRT FM

TRT FM Abokiyar sirrinku, kawarku, abokiyar tafiyarku, tana kawo shirye-shirye kai tsaye a bangarori daban-daban masu ban sha’awa kuma. Tasha ce da ta ke zuwa ko’ina ta yanar gizo da kuma tauraron dan adam.

TRT RADYO 3

TRT Rediyo 3 Tashar na kawo wakoki kala-kala tun daga na Elvis Presley zuwa Joan Baez, daga na Frank Sinatra zuwa na Tchaikowsky, daga na Mozart zuwa na Sara Vaughan. Wakoki na zamani daga Turkiyya na isa zuwa ga duniya ta yanar gizo da kuma tauraron dan adam.

TRT NAĞME

TRT NAGME Tasha ce da ke kawo wa masu sauraro zababbun wakoki daga taska da ma’ajiyar wakokin TRT. Masu sauraro na samun irin wakokin da suke sha’awar ji. Tana isa ga dukkan sassan duniya ta yanar gizo da tauraron dan adam.

TRT TÜRKÜ

TRT TURKU Tasha ce da ke kawo wa masu sauraro kalamai masu dadi, zantuttuka kyawawa kalamai daga cikin kasa, wakokin jama’a, daga masu koyo har zuwa kwararru. Tana isa ga dukkan sassan duniya ta yanar gizo da tauraron dan adam.

TRT MEMLEKETİM FM

TRT MEMLEKETIM FM tasha ce da ke kawo wa masu sauraro batutuwa da za su ba su dariya, batutuwan gudun hijira, labarai na nasara, al’adu masu kyau na kasarmu, tana kawo wakoki ga matasa masu jini a jiki. Ba ta kyale matasa haka kawai. Tashar TRT MEMLEKETIM FM tana zuwar wa masu sauraro ta tauraro dan adam da waya a kowacce rana a cikin mako da misalin karfe 9na safe zuwa 6 na yamma. Tashar ta dace da ku idan kuna son yada abubuwanda suka shafi rayuwarku ga aboka arzuka. Tashar TRT MEMLEKETIM FM n anan a tare da ku.

TRT TSR

TRT TSR Tasha ce da ke işar da shirye-shirye ga Turkawa da ke kasashen waje a cikin awanni 24. Tana bayar da ra’ayoyin Turkiyya game da batutuwan ciki da wajen kasar. Tana bayar da gudunmowa wajen tallata kasarmu, Gidan Rediyon Mruyar Turkiyya TSR na yada shiri a yaruka 31 a yau.

TRT ANTALYA

TRT ANTALYA RADIO Tun daga shekarar 1962 zuwa yau, tashar na kawo muku al’adun yankin Mediterrenean, wakoki, yanayin zamantakewa da sauransu. Acikin ranakun mako tana zuwa daga karfe 10.00 zuwa 12.00 a ranakunkarshen mako kuma karfe 12.00-12.30. bayan karfe 13.00 tana ware awa 1 don TRT Turku kuma ana kama ta a Turkiyya da duniya baki daya.

TRT ÇUKUROVA

TRT CUKUROVA RADIO Tun daga shekarar 1968 zuwa yau..tashar tana yada al’adu da salon rayuwar jama’ar Toros. A cikin mako tana kawo shiri daga karfe 10.00-12.00 a karshen mako kuma daga karfe 10.00-12.30 a garin Cukurova. Bayan karfe 16.00 tana koma wa karkashin TRT TURKU, ana kama ta a Turkiyya da duniya baki daya.

TRT RADYO GAP

TRT GAP DIYARBAKIR RADIO Tun shekarar 1964 zuwa yau, tashar tana kawo al’adun yankin kudu maso-gabashin Turkiyya, muryar rayuwar yankin,labaransu… A cikin mako tana zuwa da karfe 10.00-12.00 sai a karshen mako daga karfe 12.00-12.30. daga karfe 15.00 tana koma wa karkashin TRT TURKU, ana kama ta a Turkiyya da duniya baki daya.

TRT TRABZON

TRT TRABZON RADIO Tun daga shekarar 1968 zuwa yau ana kawo dukkan wasu batutuwa na rayuwa, al’adu da zamantakewar yankin Black Se ana Turkiyya. A cikin makotana zuwa tsakanin karfe 10.000-12.00 sai a karshen mako kuma da karfe 10.00.12.30. Bayan karfe 14.00 tana koma wa karkashin TRT TURKU, ana kama ta a Turkiyya da duniya baki daya.

TRT ERZURUM

TRT ERZURUM RADIO Tun shekarar 1960 zuwa yau tashar na kawo dukkan batutuwan rayuwa da zamantakewar yankin gabashin Anadolu. Tana kawo labarai na nishadi. A cikin makontana zuwa daga karfe 10.00-12.00 sai a karshen mako kuma tana zuwa a tsakanin karfe 10.00-12.30. A gabashin Anadolu bayan karfe 17.00 tana koma wa karkashin TRT TURKU, ana kama ta a Turkiyya da duniya baki daya.

KENT RADYO ANKARA

TRT KENT ANKARA RADIO Tana kawo duk wani batu da ya shafi birnin Ankara da abubuwan da suke faruwa. Idan kana so ka san me ke wakana a Ankara to kasance da wannan tashar. Ana kama tashar TRT KENT Ankara a kan mita 105.6 a zangon FM.

KENT RADYO İSTANBUL

TRT KENT RADIO ISTANBUL Tana kawo duk wani batu da ya shafi birnin Istanbul da abubuwan da suke faruwa. Idan kana so ka san me ke wakana a Istanbul to kasance da wannan tashar. Ana kama tashar TRT KENT Istanbul a kan mita 106.6 a zangon FM.

KENT RADYO İZMİR

TRT KENT IZMIR RADIO Tana kawo duk wani batu da ya shafi birnin Izmir da abubuwan da suke faruwa. Idan kana so ka san me ke wakana a Izmir to kasance da wannan tashar. Ana kama tashar TRT KENT Istanbul a kan mita 99.1 a zangon FM.

Radyo 6

TRT RADIO KURDI Manufar wannan tasha shi ne samar da hadin kai a tsakanin al’umar kasarmu. Tasha ce da ke yada shirye-shirye a yaren Kurdanci ga kowa da kowa. Tun ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2009 ta fara gabatar da shirye-shiryenta. Tashar ta TRT Radio 6 tana işar da muryar yankin kudu maso-gabashin yankin Anatoliya. Tana karfafa alakar al’umar yankin da kasar Turkiyya, kuma tana bayar da gudunmowa a bangaren harkokin kasa da kasa da suka shafi Turkiyya.

TRT RADYO HABER

TRT RADIO LABARAI Tasha ce da ke işar da labarai ga dukkan sassan Turkiyya. Labarai, Hasashen yanayi, Halin da Hanyoyisuke ciki, al’amura na al’adu da sana’o’i. Tana kawo wa jama’a labarai masu inganci da kayatarwa.