Ayarin farko na 'yan yawon bude ido daga Rasha sun sauka a Antalya

Ayarin farko na 'yan yawon bude ido daga Rasha sun sauka garin Antalya helkwatar yawon bude ido a Turkiyya.

1662453
Ayarin farko na 'yan yawon bude ido daga Rasha sun sauka a Antalya

Ayarin farko na 'yan yawon bude ido daga Rasha sun sauka garin Antalya helkwatar yawon bude ido a Turkiyya.

A ranar 22 ga Yuni ne Rasha ta janye dokar hana zuwa Turkiyya da ta sanya a ranar 15 ga watan Afrilu saboda annobar Corona.

Jirgin saman kamfanin Turkish Airlines dauke da fasinjoji 132 ya taso daga filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukova da ke Moscow inda ya sauka a Antalya da misalin karfe 05.40 na safiyar Talatar nan.

Bayan gama tantance matafiyan, sun shiga kananan ababan hawa tare da jakunkunansu inda suka tafi masaukansu a birnin na Antalya.

A ranar Talatar nan ana sa ran jiragen sama 44 daga Rasha za su kawo 'yan yawon bude ido sama da dubu 12 zuwa Antalya.

 Labarai masu alaka