An yi zanga-zanga a ranar 'Yan Gudun Hijira ta Duniya a Holan

A ranar 'Yan Gudun Hijira ta Duniya ta 20 ga Yuni a kasar Holan an gudanar da zanga-zanga.

1661811
An yi zanga-zanga a ranar 'Yan Gudun Hijira ta Duniya a Holan
hollanda multeciler gunu1.jpg
hollanda multeciler gunu.jpg

A ranar 'Yan Gudun Hijira ta Duniya ta 20 ga Yuni a kasar Holan an gudanar da zanga-zanga.

A zanga-zangar da aka gudanar a gabar tekun gundumar Scheveningen ta garin Lahey, an tuna da 'yan gudun hijira kimanin dubu 44 da ya zuwa yau suka mutu, an kuma rubuta sunayen wasun su tare da nunawa duniya.

A jawabin da aka gabatar an bayar da hikayoyin 'yan gudun hijirar.

An bayyana cewa, mafi yawan 'yan gudun hijirar da suka mutu a teku yayin kokarin isa zuwa Turai ba a san sunayensu ba.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, tunawa da wadanda suka mota da kokarin hana mantawa da su ba zai wadatar ba, za su ci gaba da gwagwarmaya har zai sun kubutar da rayuwar 'yan gudun hijirar.

 Labarai masu alaka