Dutsen Agri da Jirgin Ruwan Annabi Nuhu yake kansa

Ko kun san cewa dutsen Agri mafi girma a Turkiyya ya zama mai muhimmanci a Addini?

1635733
Dutsen Agri da Jirgin Ruwan Annabi Nuhu yake kansa

Dutsen Agri mai tudun mita dubu 5,137 ne mafi tsayi a Turkiyya ya zama mai muhimmanci kuma sananne saboda yadda a nan aka ajje jirgin ruwan Annabi Nuhu Alaihissalam bayan ruwan Dufana. Dutsen Agri ya zo a litattafan da aka saukar masu tsarki kuma an ambace shi a yaruka daban-daban da sunaye daban-daban. A yaren Asuriyawa an kira shi da “yankin tsaunuka”, "kasa mai tsayi” wanda asalinsa shi ne “Uruatri” wato Urartu. A yaren Ibraniyanci kuma ana ce masa “Ararat”. A yau a al’adu da dama ana kiran Dutsen Agri da sunan da ya samo daga Asuriyawa.

Fadin cewar jirgin Annabi Nuhu na kan wannan dutse na Agri ne ya sanya mutane da dama daura aniyar hawan sa. A lokacin da Marco Polo ya ce ba za a iya hawa dutsen ba a shekarar 1829 Farfesa Fredrick Von Parat ya hau shi a karon farko. Mutum na 2 da ya hau dusten kuma shi ne tsohon shugaban tarayyar masu hawa tsaunuka ta Turkiyya Dr. Bozkurt Ergor a ranar 21 ga watan 1970. Dubunnan maziyarta a kowacce shekara na ziyartar Dutsen Agri.


 


 


 Labarai masu alaka