Altun ya taya ma'aikatan rediyo murna

Shugaban Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Farfesa Fahrettin Altun ya taya murna ga dukkan ma'aikatan rediyo albarkacin Ranar Rediyo.

1635800
Altun ya taya ma'aikatan rediyo murna

Shugaban Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Farfesa Fahrettin Altun ya taya murna ga dukkan ma'aikatan rediyo albarkacin Ranar Rediyo.

Sanarwar da Altun ya fitar ta shafinsa na Twitter ta ce, shekaru 94 da suka gabata aka fara yada shirye-shirye a rediyo Turkiyya.

Ya ce, "Gidajen Rediyonmu da suka dinga kokarin hada al'umarmu waje guda na tsawon shekaru suna da muhimmanci. Ina taya murna ga dukkan ma'aikatan rediyo  Ranar Rediyo.Labarai masu alaka