Wata mace 'yar kasar Mali ta haifi jarirai 9 rigiz

Wata mace 'yar kasar Mali ta haifi 'ya'ya 9 rigiz a garin Kasabalanka na kasar Morokko.

1634346
Wata mace 'yar kasar Mali ta haifi jarirai 9 rigiz

Wata mace 'yar kasar Mali ta haifi 'ya'ya 9 rigiz a garin Kasabalanka na kasar Morokko.

Matar ta haifi mata 5 da maza 4 a lokaci guda.

Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Mali ta fitar ta bayyana cewa, Halima Sisi 'yar kasar Mali ta haihu a wani asibitin Kasabalanka bayan an yi mata tiyata.

An bayyana cewa, matar da 'ya'yanta 9 na cikin koshin lafiya.

A gwajin da aka yi wa Halima Sisi a Bamako Babban Birnin Mali an bayyana tana dauke da jarirai 7 a cikinta wanda hakan ya sanya a ranar 30 ga Afrilu ta tafi Morokko amma da ta zo haihuwa sai ta haifo jarirai 9.Labarai masu alaka