An gano wasu kaburbura masu dubunnan shekaru a Masar

A garin Dekhaliye na Masar an gano wasu tsaffin kaburbura 110 da aka samar tun kafin miladiyya.

1630131
An gano wasu kaburbura masu dubunnan shekaru a Masar

A garin Dekhaliye na Masar an gano wasu tsaffin kaburbura 110 da aka samar tun kafin miladiyya.

Ma'aikatar Yawon Bude Ido da Kayan Tarihi  ta bayyana cewa, a yayin aikin haka a Koum Al-Khulgan da ke garin Dekhaliye ne aka gano kaburburan guda 110.

An bayyana cewa, kaburbura 73 an samar da su shekaru dubu 6000-3000 kafin Miladiyya sai sauran 37 da aka samar da su shekaru 1782-1570 kafin miladiyya.

Haka zalika a kaburburan an gano alamun sassan dan adam da suka hada da kasusuwa.

 Labarai masu alaka