An kaiwa makabartar Musulmai hari a Swidin

An kai hari kan makabartar Musulmai da ke garin Malmo na kasar Swidin.

1628932
An kaiwa makabartar Musulmai hari a Swidin

An kai hari kan makabartar Musulmai da ke garin Malmo na kasar Swidin.

An birkita kaburbura 10 a yayin kai harin, kuma 'yan sanda sun fara gudanar da bincike.

Shugaban Jam'iyyar Kaloli Daban-Daban da ke Swidin Mikai Yuksel ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan hare-hare kan Musulmai na kara yawaita a Swidin.

Yuksel ya kara da cewa, hari kan makamabar Musulmai a garin Malmo abun takaici ne, kuma gwamnati da jam'iyyun siyasa ba su dauki wani matakin bayar da kariya ba.Labarai masu alaka