An kashe mutane dubu 2,444 a Mekziko

A watan Maris din da ya gabata mutane dubu 2,444 aka kashe a fadin kasar Mekziko.

1613510
An kashe mutane dubu 2,444 a Mekziko

A watan Maris din da ya gabata mutane dubu 2,444 aka kashe a fadin kasar Mekziko.

Sashen Tsaro na Tarayyar Mekziko ya fitar da rahoto game da kashe mutanen da aka yi a watan da ya gabata a kasar.

Rahoton ya ce, a watan Maris din da ya gabata an kashe mutane dubu 2,444 a kasar Mekziko wanda hakan ya zama adadi mafi yawa a wata guda tun 2011.

Ranar da aka fi kashe mutane ita ce 7 ga Maris da aka kashe mutane 103.

Haka zalika jihohin da suka fi samun yawaitar rasa rayukan su ne; Guanajuato, Michoacan, Baja Colifornia, Chihuahua da Veracruz.Labarai masu alaka