Jiragen ruwa na kasaita sun fara zuwa yankunan Bodrum na Turkiyya

Manyan jiragen ruwa na kasaita sun fara zirga-zirga a gabar tekun gundumar Bodrum ta lardin Mugla.

1446080
Jiragen ruwa na kasaita sun fara zuwa yankunan Bodrum na Turkiyya
bodrum mega yatlar1.jpg
bodrum mega yatlar.jpg

Manyan jiragen ruwa na kasaita sun fara zirga-zirga a gabar tekun gundumar Bodrum ta lardin Mugla.

Babban jirgin ruwa na kasaita mai suna "Cloudbreak" mai tsayin mita 75 da shahararrun mutane irin su Jennifer Lopez, Heidi Klum, Julia Roberts da sauransu suke yin hutu a cikinsa ya zo unguwar Yalikavak da ke gabar tekun Bodrum tare da tsayawa.

An gano jirgin ruwan na d kyau kuma an samar da shi da fari da bakin karfe, wanda kuma yana da ikon zuwa kowacce gabar teku kuma a kowanne irin hali.

A cikin jirgin ruwan akwai jirgin sama mai saukar ungulu, wuraren wanka da ninkaya, Jakuzi, dakunan wasanni, gidan sinima da sauran kayan more rayuwa.

Wani jirgin ruwan na kasaita mai dauke da tutar Cayman ma ya zo gabar tekun ta Bodrum.

Jiragen ruwan da ba a san ko su waye a ciki ba na jan hankali sosai.Labarai masu alaka