Tsohon garin Kanlidivane a Turkiyya ya shirya tarbon ‘yan yawon bude ido

An sanar da cewa garin Kanlidivane dake karkashin gundumar Erdemli ya shirya tsaf domin tarbon ‘yan yawon bude ido ciki da waje

1444934
Tsohon garin Kanlidivane a Turkiyya ya shirya tarbon ‘yan yawon bude ido

An sanar da cewa garin Kanlidivane dake karkashin gundumar Erdemli ya shirya tsaf domin tarbon ‘yan yawon bude ido ciki da waje.

An kaddamar da shirye-shiryen kanfen din garin Kanlidivane da aka yiwa lakabi da “boyayyar aljanna”

Tsohon garin ya kasance tun lokacin karni na 13 wanda keda gidaje da suka hada da na duwatsu, manyan duwatsu da kanfunan sarrafa man zaitun.

Kandlidivane dake yankin Kizkalesi akan iyakar madeterrenian ya kasance daya daga cikin yankun dake cikin littafin al’adun hukumar UNESCO.

Magajin garin Erdemli, Mükerrem Tollu ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Abnadolu da cewa an dauki dukkanin matakai domin tarbon ‘yan yawan bude ido zuwa yankin da kuma ta yadda za’a kare kowa daga annobar da ake cigaba da kalubalanta.

 

 Labarai masu alaka