Turkiyya na cigaba da tallafawa kasashe a yaki da Covid-19

Kasar Turkiyya na cigaba da tallafawa kasashe da dama a yaki da sabuwar kwayar cutar Covid-19; inda ta aike da wasu karin kayyakin kiwon lafiya zuwa Sudan da Uganda

1444310
Turkiyya na cigaba da tallafawa kasashe a yaki da Covid-19

Kasar Turkiyya na cigaba da tallafawa kasashe da dama a  yaki da sabuwar kwayar cutar Covid-19; inda ta aike da wasu karin kayyakin kiwon lafiya zuwa Sudan da Uganda.

Hukumar Hadin Kai da Bayar da Tallafi ta kasar Turkiyya watau TIKA, shugabanta na Sudan Bilal Ozden ya bayyana cewar kayan agajin da suka hada da takunkuman rufe fuska da sauran kayayyakin kiwon lafiya da aka aiko dasu daga Turkiyya an mikasu ga jami'an gwamnatin Sudan a Hartum babban birnin kasar.

Özden, ya kara da cewa a kwanakin baya ma an bayar da gudunmowar da aka aiko daga Turkiyya da suka hada da takunkuman rufe fuska ga asibitin koyarwar jihar Niyala da kuma ma'aikatun lafiyar dake Gabashin Darfur.

A gefe guda kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta  Türk Kızılay ta tallafawa abokiyar aikinta ta Uganda da kayayyakin kiwon lafiya domin tallafawa mabukata.

An mika kayayyakin ga shugaban hukumar Red Cross ta kasar Uganda Robert Kwetsiga a Kampala babban birnin kasar.  Jakadan Turkiyya a Uganda Fikret Kerem Alp ya bayyana cewa wannan gudunmowar kayayyakin taimakawa Uganda domin yaki da Corona na jin kai ne.

 Labarai masu alaka