'Yan yawon bude ido sun fara ziyartar tsibirin Cunda dake Turkiyya

An bayyana cewa tsibirin Cunda (Alibey) ɗaya daga cikin cibiyoyin yawon shakatawa na Arewacin Aegean a kasar Turkiyya, ya fara karbar bakuncin masu yawon shakatawa na gida da na waje a guraren shakatawan gidajen Girka, majami'u da otal-otal

1430705
'Yan yawon bude ido sun fara ziyartar tsibirin Cunda dake Turkiyya

An bayyana cewa tsibirin Cunda (Alibey) ɗaya daga cikin cibiyoyin yawon shakatawa na Arewacin Aegean a kasar Turkiyya, ya fara karbar bakuncin masu yawon shakatawa na gida da na waje a guraren shakatawan gidajen Girka, gidajen katako, majami'u da otal-otal.

Daga cikin tsibiran 22 na Ayvalık, gundumar Balıkesir, wanda aka bayyana da "Island City", ya kasance daya daga cikin tsibirin Cunda da Lale.

Tsibirin Cunda, wacce hanyace ta isa  Ayvalık zuwa gadar Bosphorus wacce aka bude a shekarar 1964, tana cikin manyan cibiyoyin yawon shakatawa na Edremit Bay dake Arewacin Aegean.

Kasancewar yadda yanayin zafin tsibirin Cunda yake da kuma tsirai da dama ya sanya yankin kasancewa mai muhunmmanci ga 'yan yawon bude ido.

 Labarai masu alaka