An dawo da yawon bude ido a jiragen ruwa a Antalya

A yankin Antalya na Turkiyya, an bayar da damar a fara yawon bude ido na kwana guda a teku a kan kananan jiragen ruwa.

1428388
An dawo da yawon bude ido a jiragen ruwa a Antalya

A yankin Antalya na Turkiyya, an bayar da damar a fara yawon bude ido na kwana guda a teku a kan kananan jiragen ruwa.

Mahukuntan yankin sun bayyana cewar a yanzu an bayar da damar a dawo da harkokin yawon bude idon a kan teku da jiragen ruwa kanana, wanda a baya saboda annobar Corona (Covid-19) aka dakatar.

An bukaci masu jiragen ruwan da su kula sosai wajen tsafta da kare kawunansu da jama'ar da za su dauka.

 Labarai masu alaka